Iyalan Shahid Fakhrizadeh Sun Karbi Kyautar Yabo Ta “Nsar” A Jiya Lahadi

2020-12-14 10:18:19
Iyalan Shahid Fakhrizadeh Sun Karbi Kyautar Yabo Ta “Nsar” A Jiya Lahadi

Babban hafsan hafsoshin sojan Iran Manjo Janar Muhammad Bakiri ne ya kaddamar da lambar yabon ga iyalan na masanin fasahar Nukiliya wanda aka yi wa kisan gilla makwanni kadan da suka gabata, a matsayin jinjinawa a gare shi danage da rawar da ya taka wajen ci gaban Iran.

Lambar yabo ta “Nasr” tana a matsayin lamba mafi girma ta sojojin Iran.

Gabanin shahdar tashi, Dr. Fkahrizadeh ya kasance mataimakin ministan tsaro na Iran, kuma shugaban cibiyar bincike da kirkira da ke karkashin ma’aikatar tsaron, wanda jagoran juyi ya bayyana shi da cewa; Masanin ilimin kimiyya ne na musamma da kuma harkar tsaro.”

An yi masa kisan gilla ne da marecen wata juma’a ta 27 ga watan Nuwamba a kusa da garin Absard dake gabashin Iran.

Iran ta zarfi HKI da yi wa masanin kisan gilla, ta kuma yi alkawalin daukar fansa akan kisan nashi.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!