Shugaban Aljeriya Ya Bayyana Bayan Shafe Dogon Lokaci Na Jinya

2020-12-13 19:27:45
Shugaban Aljeriya Ya Bayyana Bayan Shafe Dogon Lokaci Na Jinya

Shugaban kasar Aljeriya, Abelmadjid Tebboune, ya bayyana a gidan talabijin din kasar a wani jawabi da ya yi wa al’ummar kasar a yau Lahadin.

A cikin jawabin nasa shugaban ya bayyana cewa zai ci gaba da jinya ta tsawon makwannin biyu zuwa uku.

Marabin da a ga shugaban bainar jama’a tun ranar 15 ga watan Oktoba da ya gabata, sakamakon killace kansa da kuma jinyar da ya yi ta cutar korona a kasar Jamus.

Shugaban kasar dai ya yi jamwabi ne a jajibirin cikarsa shekara guda samun nasara a zaben shugabancin kasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!