Arewacin Nigeria Yana Fuskantar Yunwa Saboda Hare-haren Da Ake Kai Wa

2020-12-13 14:53:09
Arewacin Nigeria Yana Fuskantar Yunwa Saboda Hare-haren Da Ake Kai Wa

Shugaban kungiyar manoma na jahar Sokoto Dr. Murtala Gagadu ya shaidawa jaridar Vanguard da ake bugawa a Nigeria cewa; Da akwai wasu yankuna da kokadan manoma ba za su iya zuwa ba a cikin daji da gonaki.

Dr. Murtala ya kuma bayyana cewa manoman jihar ta Sokoto sun shuka ridi a cikin gonakin da girmansu ya haura eka 40, da lokacin girbi ya zo, masu dauke da bindiga sun zo su ka rika yin garkuwa da manoma.

Har ila yau shugaban kungiyar manoman ta jihar Sokoto ya ce; Masu dauke da makaman sun taba kafawa mazauna karkara sharadin cewa idan ba su son a sace musu dabbobi da amfanin gona to kowane gida ya bayar da yaro guda da zai zama wakilinsu a cikin rundunar ta barayi a rika sata da shi.”

Wasu jihohin da suke fuskantar yanayi irin na Sokoto, su ne Borno, katsina, Niger, Zamfara, Gombe, Kaduna da kuma Plateau, inda kai da komawar masu dauke da makamai a cikinsu su ke barazarar fuskantar karancin abinci.

Da dama daga cikin manoma a wadannan jihohin dai sun kauracewa gonakin nasu saboda tsoron kisa.

Babu wata kididdiga akan adadin manoman da aka kashe a cikin wannan shekara ta 2020 kadai, wanann wasu alkaluman suna cewa sun kai dubbai.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!