“Yan Sandan HKI Sun Jikkata Mutanen Tuddan Gulan Da Dama A Yau Laraba

2020-12-09 19:39:39
 “Yan Sandan HKI Sun Jikkata Mutanen  Tuddan Gulan Da Dama A Yau Laraba

“Yan Sandan HKI Suna Jikkata Mutanen Tuddan Gulan Da Dama A Yau Laraba

Mutanen yankin na tuddan Gulan da yake a karkashin mamayar ‘yan sahayoniya suna nuna kin amincewarsu da shirin kafa manyan fankokin samar da makamashi a cikin gonakinsu ba tare da izininsu ba.

An gudanar da yajin aiki da dukkanin wuraren aiki da makarantu dake yankin na tuddan Gulan, sannan kuma mutanen sun yi cincirindo da zaman drishan a cikin gonakin nasu.

“Yan sandan HKI sun yi amfani da kulale da kuma hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa mutanen da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar da dama daga cikinsu.

Al’ummar yankin na tuddan Gulan da larabawa ne sun yanke shawarar yin yajin aikin ne bayan wani taro da shugabannin addini da na al’umma su ka yi.

Tun shekaran jiya Litinin ne dai ‘yan sahayoniyar su ka killace hanyoyin da suke shiga cikin kauyukan na tuddan Gulan.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!