​Shugaban Masar Ga Macron: Addinin Ubangiji Hurumi Ne Mai Tsarki Da Daraja

2020-12-09 09:20:33
​Shugaban Masar Ga Macron: Addinin Ubangiji Hurumi Ne Mai Tsarki Da Daraja

Shugaban kasar Masar Abdulfattah Al sisi ya sheda wa Macron na Faransa cewa, abubuwa da suke da alaka da ubangiji suna da tsarki da kuma daraja.

Tashar Almanar ta bayar da rahoton cewa, a ganawar da ta gunada tsakanin shugaban Masar Abdulfattah Al sisi da kuma shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron a ziyarar da ya kai a kasar a ranar Litinin da ta gabata, ya sheda wa Macron cewa, kada ku fake da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki, kuna bakantawa daruruwan miliyoyin mutane.

Shugaban na Masar ya ce da Macron, addini da akida da sauran abubuwa da suke da alaka da ubangiji, abubuwa ne da suke a birbishin kowane dan adam komai matsayinsa, domin mutane su ne baiwa dan adam wani matsayi na duniya, amma matsayi wanda Allah ne ya daukaka annabawa da shi, babu wani mahaluki da zai iya kai wag a wannan matsayin balanta ya ci zarafi ko yin tozarci a kansa da sunan ‘yancin fadar albarkacin baki.

A nasa bangaren shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ya mayar da nasa bayanin da cewa, abin da musulmi suke magana a kansa na zanen batunci ga ma’aiki ba gwamnatin Faransa ce ta yi hakan ba, wata jarida ce mai zaman kanta, saboda lamarin ba shi da wata alaka da gwamnatin Faransa.

Tun bayan nuna zanen batuncin da aka yi a kan Faransa a baya-bayan nan a kan ma’aiki Macron ya fito ya kare masu yin zanen, tare da bayyana cewa suna damar yin hakan kamar yadda dokar kundin tsarin mulkin Faransa ta yarje musu.

015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!