Iran Ta Shirya Kara Yawan Man Da Teka Hakowa Da Kuma Fitarwa

2020-12-08 10:16:26
Iran Ta Shirya Kara Yawan Man Da Teka Hakowa Da Kuma Fitarwa

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani ya sanar da cewa, kasarsa ta shirya kara yawan albarkatun man da take hakowa da kuma fitarwa zuwa ketare.

Kamfanin dillancin labaran kasar IRNA ya ruwaito shugaba Rouhanin yana bayyana cewa, karfin aikin hako man da Iran ke da shi, gami da kwarewarta a fannin, ya sanya kasar ke fatan gaggauta kara yawan man da take hakowa da kuma yin cinikinsa.

Yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015, ta baiwa Iran damar fitar da sama da ganga miliyan 2 na danyen man kafin Amurka ta dauki mataki na kashin kanta na sanya takunkumi kan Iran a shekarar 2018, kamar yadda shugaba Rouhani ya bayyana.

M. Rouhani ya bayyana a lokacin taron rukunin hukumomin kula da tattalin arzikin kasar cewa, ma’aikatar kula da albarkatun man kasar Iran an dora mata alhakin daukar dukkan shirye shiryen da suka dace domin ganin kamfanonin samar da mai na kasar su kai matakin cinikinsa, gwargwadon karfin samar da man da kasar ke da shi, nan da watanni uku masu zuwa.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!