MDD Ta Damu Da Halin Da Ake Ciki A Yankin Tigray Na Habasha

2020-12-08 10:11:08
  MDD Ta Damu Da Halin Da Ake Ciki A Yankin Tigray Na Habasha

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana damuwa matuka game da halin da ake ciki yanzu a yankin Tigray na kasar Habasha, inda dakarun gwamnati ke fafatawa da mayakan ‘yan tawayen yankin.

Cikin wata sanarwa da kakakinsa Stephane Dujarric ya fitar, jami’in na MDD ya ce, wajibi ne a gaggauta dawo da doka, da kare hakkoki na dan Adam, da sake dawo da harkoki, da bude hanyoyin kaiwa ga masu bukatar taimakon jin kai.

Ya kuma nanata kudirin MDDr na goyon bayan yunkurin kungiyar tarayyar Afirka, da samar da taimakon jin kai ga ‘yan gudun hijira, da wadanda rikicin ya raba da muhallansu gami da daukacin mutanen dake cikin matsi.

Rahotanni daga arewacin Tigray na cewa sojojin Habasha sun dakatar da jami'an Majalisar Dinkin Duniya daga shiga wani sansanin 'yan gudun hijira.

Wasu rahotanni da ba a tabatar ba na cewa an harbi daya daga cikin jami'an MDD a ranar Lahadi a daidai lokacin da tawagar ta majalisar ke kokarin shiga sansanin da ke a Shimelba, wanda mazauni ne ga dubban 'yan Eritrea.

Wannan na zuwa ne kwana daya bayan MDD ta bayyana cewa ta cimma matsaya da hukumomi a Habasha domin kai kayan agaji a yankin Tigray wanda a halin yanzu ke karƙashin gwamnatin tarayyar kasar bayan shafe sama da wata guda ana rikici.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!