Kwallon Kafa: Har Yanzu Makomar Lionel Messi Na Cike Da Sarkakiya

2020-12-07 10:15:32
Kwallon Kafa: Har Yanzu Makomar Lionel Messi Na Cike Da Sarkakiya

Kasantuwar cewa ga alamu dai burin dan wasa Messi na barin Barcelona a farkon wannan kakar bai cika ba amma ana ganin lokaci yayi da dan wasan zai fara tattaunawa da wasu daga cikin kungiyoyin da suke bibiyarsa.

Sai dai a kwanakin baya kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dake Ingila tace ta hakura da zawarcin da take yiwa dan wasan bayan da kungiyar tayi lissafin irin kudin da zata kashe a lokacin yin cinikin.

A cikin watan Agustan daya gabata kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta so daukar dan wasa Lionel Messi daga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, bayan da dan kwallon ya bukaci barin kungiyar sakamakon rashin jituwa da tsohon shugaban gudanarwar ta Barcelona.

Barcelona ta ci karo da cikas a kakar bara, bayan da ta kasa lashe kofi ko guda daya, bayan dukan kawo wuka da Bayern Munich ta yi mata a gasar cin kofin zakarun turai 8-2.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!