​Sudan: jam’iyyar Umma Ta Zargi Gwamnatin Rikon Kwarya Da Kasa Tabuka Komai Ga Al’ummar Kasa

2020-12-07 09:45:32
​Sudan: jam’iyyar Umma Ta Zargi Gwamnatin Rikon Kwarya Da Kasa Tabuka Komai Ga Al’ummar Kasa

Jam’iyyar Umma ta marigayi Sadiqul Mahdi ta zargi gwamnatin rikon kwaryar kasar Sudan da kasa tabuka komai ga al’ummar kasar.

Jam’iyyar Umma a kasar Sudan, ta bayyana halin ko in kula da mahukuntan gwamnatin rikon kwaryar kasar suke nuanwa dangane da bukatun al’ummar kasar da cewa lamari ne mai matukar hadari.

A cikin bayanin da jam’iyyar ta fitara jiya Lahadi ta bayyana cewa, tun bayan da sabbin mahukuntan suka karbi ragamar tafiyar da lamurran gwamnatia kasar, ya zuwa babu abin da suka tsinana ma kasar, in banda kokarin burge kasashen ketare.

Bayanin ya ce al’ummar da suka kawar da gwamnatin Albashira Sudan suna nan, kuma ci gaba da nuna halin ko in kulak an bukatun al’ummar kasa, zai iya sake haifar da abin da sabbin mahukuntan ba su yi zato ba.

Jam’iyyar Umma na daga cikin jam’iyyun siyasar kasar Sudan da suka nuna rashin amincewa da kulla alaka da gwamnatin yahudawan Isra’ila da sabbin mahukuntan kasar ta Sudan suka yi, bisa matsin lamabar gwamnatocin Amurka da Saudiyya da kuma UAE.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!