Ministan Harkokin Wajen Kasar Siriya Zai Kai Ziyarasa Ta Farko zuwa Kasashen Waje A Kasar Iran

2020-12-06 21:13:50
Ministan Harkokin Wajen Kasar Siriya Zai Kai Ziyarasa Ta Farko zuwa Kasashen Waje A Kasar Iran

Faisal Mikdad sabon ministan harkokin wajen kasar Siriya zai fara ziyarar farko zuwa kasashen waje tun bayan da aka nada shi a wannan mukamin, kuma zai fara ziyarar ce da kasar Iran. Ana kuma sa ran zai gana da takwaransa na kasar Iran Jawad Zarfi da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar domin tattaunawa game da muhimman batutuwa da suka shafi kasashen biyu.

A ranar 22 ga watan Nuwamba da muke ciki ne aka nada Faisal Mikdad a matsayin sabon ministan harkokin wajen kasar ta Siriya domin maye gurbin tsohon ministan Walid Mua’llim da Allah yayi wa rasuwa a yan kwanakin baya.

A ganawarsa da jakadan Iran a kasar ta Siriya, Mikdad ya yi tir da kisan da aka yi wa masanin ilimin nukiliya na kasar Iran Mohsen Fakhrizade , kuma ya nuna cewa Iran tana da karfin dakile irin wannan harin na ta’adancin da HKI ke jagoranta.

Daga cikin mukaman da ya rike a baya, da akwai wakilin kasar siriya na din din din a a MDD daga shekarun 2003 zuwa 2006


Comments(0)
Success!
Error! Error occured!