Faransa : Ana Ci Gaba Da Zanga-zangar Adawa Da Dokar Tsaro
2020-12-06 09:50:52

A Faransa, ana ci gaba da zanga zangar adawa da dokar tsaro, inda ko a jiya Asabar ma dubban masu zanga zangar ne suka fito a sassa daban daban na kasar, domin nuna kyama ga dokar data tanadi hana yada hotunan ‘yan sanda lokacin da suke kan aiki.
Alkalumman da ma’aikatar cikin gidan faransar ta fitar sun ce an samu mutane sama da dubu hamsin da suka shiga zanga zangar, daga cikin 5,000 sun kasance ne a birnin Paris.
Saidai zanga-zangar ta rikide a wasu sassan kasar inda arangama ta barke tsakanin jami'an tsaro da masu zanga zangar.
Rahotanni daga kasar sun ce an farma wa manyan shaguna da dukiyoyin jama'a da bankuna, yayin da aka kona motoci da dama.
Masu
zanga-zangar sun yi ta jifan yan Sanda da duwatsu, yayin da su kuma suke harba
musu hayaki mai sa hawaye.
024
Tags:
faransa
ana ci gaba da zanga zangar adawa da dokar tsaro
dokar data tanadi hana yada hotunan ‘yan sanda
sakanin jami'an tsaro da masu zanga zangar.
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!