Majalisar Dokokin Mali Ta Zabi Soja A Matsayin shugaba

2020-12-06 09:45:26
Majalisar Dokokin Mali Ta Zabi Soja A Matsayin shugaba

Majalisar dokokin kasar Mali ta zabi daya daga cikin sojojin da suka kifar da mulkin tsohon shugaba Ibrahim Boubacar Keita, a matsayin shugaban ta.

Majalisar mai dauke da kujeru 121 da suka kunshi Yan siyasa da wakilan kungiyoyin fararen hula da kungiyoyin kwadago da kuma sojoji sun zabi Kanar Malick Diaw a matsayin shugaba a zaman farko data gudanar.

Yan Majalisu 108 suka zabi Kanar Diaw wanda ya tsaya takara ba tare da hamayya ba.

Bayan zabensa, kanar Diaw, ya yi alkawarin yin aiki tukuru domin hada kan al’ummar kasar ta Mali, da kuma cimma maradun kasar.

Majalisar CNT, dai it ace zata maye gurbin majalisar dokokin kasar a mulkin rikn kwarya, kuma mambobinta sun kasance ne tamakar ‘yan majalisar dokoki amma ba wadanda aka zaba ba.

Kafa majalisar dai ya kawo karshen kwamitin kasa na CNSP, da sojoji suka kafa bayan hambarar da mulkin IBK, a ranar 18 ga watan Agusta da ya gabata.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!