An Fara Allurar Rigakafin Cutar Korona A Kasar Rasha
2020-12-05 14:30:55

A wani lokaci yau Asabar ne ake fara yi wa mutane allurar riga kafin cutar korona a kasar Rasha.
Bayanai daga Rashar sun ce tuni asibitoci a Moscow babban birnin kasar, suka kimsa domin fara yi wa mutane allurar ta korona mai suna Sputnik V, kamar yadda shugaban kasar Vladimir Putin ya bada umarni.
Za’a dai fara yi wa mutanen da suka fi hadarin kamuwa da cutar allurar, da suka hada da ma’aikatan lafiya.
Bayanai da masu samar da
rigakafin na Rasha suka fitar sun ce tasirinsa ya kai kashi 95 cikin 100,
sannan kuma ba ya haifar da wata babbar illa.
024
Tags:
rasha
korona
allurar riga kafin cutar korona
vladimir putin ya bada umarni
allurar ta korona mai suna sputnik v
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!