Iran Ta Bayyana Cewa: Zargin Da Amurka Ta Ke Yi Ma Ta Ba Shi Da Wata Kima A Wurinta

2020-11-20 14:08:37
Iran Ta Bayyana Cewa:  Zargin Da Amurka Ta Ke Yi Ma Ta Ba Shi  Da Wata Kima A Wurinta

Jakadan Jamhuriyar Musulunci ta Iran a hukumar makamashin Nukiliya ta kasa da kasa Kazim Gharibabady ya fada a jiya Alhamis a yayin taron kwamitin alkalai na hukumar makamashin ta kasa da kasa wanda aka yi ta hanyar bidiyo daga nesa cewa;

"Maganar da wakilin Amurka a hukumar ya yi abinda dariya ne."

Shi dai wakilin na Amurka a hukumar makamashin Nukiliyar ta kasa da kasa ya bayyana cewa; Wajibi ne a rika yi wa Iran bincike da sanya idanu na koli.

Wakili na Iran ya ce; Shin abinda Amurkan take nufi shi ne a rika yi wa Iran din bincike kamar yadda ake yi ma ta? Ko kuwa take dokokin kasa da kasa kamar yadda ita yi?

Gharibabady ya kuma ce; Shugabannin hukumar makamashi ta kasa da kasa da suka gabata da na yanzu duk sun amince da cewa ana yi wa Iran bincike na koli, amma idan Amurka tana nufin akwai wani tsarin na daban, sai ta gabatar da hukumar, idan ta amince sai a ayi aiki da shi.

013

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!