Janar Salami: Don Tabbatar Da Tsaron Kasarta, Iran Ba Za Ta Takaita Kanta Da Wani Yanki Ba

2020-11-19 21:35:52
Janar Salami: Don Tabbatar Da Tsaron Kasarta, Iran Ba Za Ta Takaita Kanta Da Wani Yanki Ba

Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin Musulunci na kasar Iran (IRGC) Manjo Janar Hossein Salami ya bayyana cewar Iran ba za ta taba takaita kanta da wani yanki ba wajen mayar da martani ga duk wani wuce gona da iri da aka yi mata.

Janar Salami ya bayyana hakan ne a yayin da yake gabatar da jawabi a yau din nan Alhamis yayin mika wani sabon jirgin ruwan yaki da masanan Iran suka kera wa dakarun na IRGC inda ya ce: Ba za mu taba takaita kanmu da wani yanki wajen kare kanmu da kuma manyan manufofinmu ba. Don haka duk wanda yake son yin barazana ga manufofin wannan al’umma da kuma wannan kasa ta mu mai girma, to kuwa lalle ba zai sami mafaka a duk fadin duniyar nan ba.

Har ila yau, babban kwamandan dakarun IRGC din ya sake jaddada cewa babbar siyasar Iran ita ce kare kanta daga barazanar makiya, don haka Iran ba ta barazana ga wata kasa ba, to sai dai kuma a kullum wannan siyasar kariyar tana tafe da shirin ko ta kwana na mayar da martani ga duk wata barazana.

A wani bangare na jawabin nasa, Janar Salami ya ce yankin Tekun Fasha wani jigo ne na tsaron kasar Iran, don haka kamata yayi duniya ta jinjinawa Iran da kuma dakarun kasar Iran saboda irin yadda suka tabbatar da tsaron wannan yanki mai matukar muhimmanci ga tsaro da kuma tattalin arzikin duniya.

014

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!