​‘Yan Majalisa: Lokaci Ya Yi Da Za A Kori Hafsoshin Tsaro A Najeriya

2020-08-01 09:37:13

Jaridar Daily Trust ta bayar da rahoton cewa, wasu daga cikin ‘yan majalisar wakilai sun jaddada kira ga Shugaba Buhari da ya sallami manyan hafsoshin tsaro, sakamakon harin ‘yan Boko Haram a kan Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno.

Shugaban Marassa Rinjaye na Majalisar, Ndudi Elumelu, ya ce lokaci ya yi da Buhari zai aiwatar da matsayar Majalisun Tarayya, da ke neman ya tasa keyar manyan hafsoshin saboda sun gaza.

Elumelu ya bayyana kaduwa kan harin da mayakan suka kai a kan ayarin motocin gwamnan Borno, yana mai cewa wajibi ne a gaggauta sauya shugabancin rundunar tsaron Najeriya.

Yin hakan a cewarsa shi ne zai taimaka a magance matsalar tsaron Najeriya yadda ya kamata.

Elumelu ya ce sabbin manyan hafsoshin tsaro za su kawo sabbin dabaru da karin himma wajen kawar da matsalar.

A ranar Laraba mayakan Boko Haram suka kai wa gwamnan hari a hanyarsa ta kai wa ‘yan gudun hijira abinci.

Karo na biyu ke nan da kungiyar ta yi yunkurin kai masa hari, lamarin da ya kara fusata shi.

Gwamnan na Borno ya sha kalubalantar sojoji kan gazawarsu wajen kawo karshen hare-haren kungiyar a jihar.


Tags:
Comments(0)