Kasar Sin Ta Ce; Birtaniya Ba Ta Da Makoma Mai Kyau Idan Ta Ci Gaba Na Fada Da Ita

2020-07-31 20:59:45

Kasar ta China ta ja kunnn Birtaniya ne akan ta daina halayyar da take nuna mata wacce ta yi matukar gurbata alakar kasashen biyu.

Wanann gargadin na kasar Sin akan Birtaniya ya biyo bayan matakin da Fira ministan Birtaniya Borsi Johnson ya dauka na hanawa kamfanin Huwei na Sin, shiga cikin aikin kafa hanfoyin sadarwa na G5.

Jakadan kasar Sin a London Leo Shiu Ming ya fadawa manema labaru cewa; :Wasu daga cikin ‘yan siyasar Birtaniya suna gurbata alakar Sin da Birtaniya ta hanya mafi muni,domin a cikin kwakwalensu da akwai tunanin yanin ruwan sanyi.”

Bugu da kari jakadan na kasar Sin ya zargi wasu ‘yan siyasar na Birtaniya da cewa suna yi wa Sin barazana domin sun dauke ta a matsayin abokiyar gaba, har ta kai suna yin Magana da bude sabon yakin ruwan sanyi da kasar Sin.

Jakadan na kasar Sin ya kuma cewa; Da wuya a ce Birtani tana da makoma a duniya anan gaba, idan har ta ci gaba da nesanta kanta daga China, domin rabuwa da China yana nufin rabuwa da ci gaba.” Kamar yadda ya fada.

A Karon farko tarayyar turai ta kakaba wa wasu mutane shida na China da Rasha takunkumi bisa zarginsu da hannu akan kutsen internet.

Tags:
Comments(0)