Masu Cutar COVID-19 A Afrika Sun Zarce 92,000

2020-05-21 22:35:00

Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta Afrika (Africa CDC), ta ce adadin mutanen da suka kamu da annobar COVID-19 a Afrika ya kai 92,348.

A Alkalumanta na baya bayan nan cibiyar ta kuma ce yawan mutanen da suka mutu sakamakon cutar COVID-19 a Afrika ya karu daga 2,918 a yammacin ranar Laraba.

Haka zalika cibiyar ta Africa CDC ta sanar cewa kimanin mutane 36,117 sun warke daga cutar COVID-19 a fadin nahiyar, inda aka samu sabbin mutanen da suka warke daga cutar kimanin 2,002 cikin sa'o'i 24.

Rahoton na Africa CDC ya nuna cewa, annobar ta yadu a dukkan fadin nahiyar, kuma kasashen da annobar ta fi kamari sun hada da Afrika ta kudu mai adadin mutane 17,200 da suka kamu da cutar, sai Masar mai mutane 13,484 a Algeriya kuwa mutum 7,377ne suka kamu da cutar, yayin da kasar Morocco aka samu mutane 7,023 da suka kamu da cutar.

Tags:
Comments(0)