Venezuella Za Ta Yi Rakiyar Jiragen Dakon Man Iran

2020-05-21 22:34:03

Kasar Venezuella, ta sanar da cewa za ta yi rakiyar jiragen dakon man fetur na Iran da zasu kai mata man fetur.

A halin da ake ciki dai jiragen ruwan dakon man Iran guda biyar ne suka kama hanyar zuwa Venezuella, domin kai man fetur da ake fuskantar karancinsa yau sama da watanni biyu a kasar ta Venezuella.

Kasashen biyu dai sun gargadi Amurka da kada ta kuskura ta kawo cikas ga jigilar man fetur din.

Shugaban kasar Venezuella dai Nicolas Maduro, ya dora alhakin karancin man da ake fuskanta a kasarsa ga Amurka data kakaba wa kasar takunkumi.

Mista Maduro, ya kuma goda wa Iran, akan wannan kokarin na kai man fetur a kasarsa.

Amurka dai ta fusata kan kusancin dake tsakanin kasashen biyu, wadanda dukkaninsu ke fuskantar takunkumanta.

Ministan tsaron kasar Venezuellar, ya ce jiragen dakon man na Iran zasu samu rakiya sojoji da zarar sun shigo cikin ruwan kasar ta Venezuella, a yayin da ita kuwa Iran ta gargadi Amurka akan duk abunda zai biyo baya, idan ta kuskura ta kawo wa jiragen nata cikas.

Tags:
Comments(0)