Za’a Yi Zana’izar Paparoma Francis A Ranar Asabar 26 Ga Watan Afrilu

Majiyar fadar Vatican ta bada sanarwan cewa za’a gudanar da jana’izar paparuma Francis a ranar Asabar mai zuwa 26 ga watan Afrilu a dandalin st.

Majiyar fadar Vatican ta bada sanarwan cewa za’a gudanar da jana’izar paparuma Francis a ranar Asabar mai zuwa 26 ga watan Afrilu a dandalin st. Peter dake birnin Vatican amma za’a ajiye gawarsa don yi mata kallo na karshe a daga gobe Laraba a St. Peter’s Basilica har zuwa ranar Jana’izar.

Shafin yanar gizo na labarai “Africa News” ya bayyana cewa paparoma Francis ya mutane a ranar 20 ga watan Afrilu yana dan shekara 88 a duniya, kuma fatansa a cikin jama’a da kuma jawabinda na karshe kwana guda ne kafin rasuwarsa.

Labarin ya kara da cewa paparoman ya shahara da son talaka, da kuma wadanda aka zalunta, musamman al-ummar Falasdinu, wadanda yahudawan HKI suke yiwa kissan Gila tun sdhekara ta 2023.

Cardinal-cardinal na catholica sun fara taro a Vatican a yau Talata don neman wanda zai gajesi a cikinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments