Mutane 47 ne suka rasa rayukansu tare da jikkatan wasu da dama a harin da aka kai da jirgin sama kan birnin El-Fasher na kasar Sudan
Runduna ta 6 da ke yankin El- Fasher ta sanar da mutuwar fararen hula 47 tare da jikkata wasu da dama sakamakon kazamin lugudan wuta da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suka yi kan birnin El- Fasher, fadar mulkin jihar Darfur ta Arewa.
A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce: Dakarun Kai Daukin Gaggawa na Rapid Support Forces na ci gaba da kai hare-hare kan fararen hula, inda suka yi amfani da harsasai masu yawa a yayin da suka yi ruwan wuta a kan unguwannin birnin El-Fasher a wannan mako, inda suka kashe fararen hula 47, ciki har da mata 10, wadanda hudu daga cikinsu sun kone a cikin gidajensu. Sannan an kashe mata hudu a wani bangare, yayin da mata biyu an kashe sune a lokacin da suke tafiya.