Jami’an tsaron kasar Iran sun sanar da mutuwar madugun kungiyar data dauki alhakin kai harin Taftan wanda a yayinsa ‘yan sanda kasar akalla goma sukayi shahada.
Mai Magana da yawun ‘yan sandan kasar Birgediya Janar Saeed Montazer al-Mahdi a ziyarar da ya kai lardin Sistan da Baluchestan ya bayyana cewa, “Mun cika alkawarin da muka dauka na neman adalci ga jinin jami’an ‘yan sandan mu da suka yi shahada.”
An gano shugaban ‘yan ta’addar ne a yankin Goharkouh a gundumar Taftan, bayan wani gagarumin samame da jami’an ‘yan sanda na yaki da ta’addanci suka yi.
Montazer al-Mahdi ya bayar da rahoton cewa, a cikin sa’o’i 24 da suka gabata an kama wasu ‘yan ta’adda biyu, daya daga cikinsu ya dauki hoton inda aka kai harin kuma zai fuskanci shari’a.
An tsare wasu mutane 6 da ke goyon bayan ‘yan ta’addar, tare da amsa laifinsu na kisan jami’an ‘yan sanda a shekarun baya-bayan nan.
An kai harin ne a daidai lokacin da jami’an ‘yan sanda ke dawowa daga kiran gaggawa da akayi musu a yankin na Taftan, inda nan ne ‘yan ta’addan sukayi musu kwanton-bauna.