‘Yan majalisar dokokin Aljeriya sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila

‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila. ‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman

‘Yan majalisar dokokin Aljeriya, sun yi kira da a haramta daidaita alaka da Isra’ila.

‘Yan majalisar dokokin Aljeriya da wakilan jama’a na kasar a zaman majalisar dokokin kasar, sun yi Allah wadai da laifukan da Isra’ila ke aikatawa akan al’ummar Gaza, tare da nuna cikakken goyan bayansu ga falasdinawa.

Mahalarta taron sun yi kira ga majalisar dokokin kasar da ta yi amfani da dokar da ta haramta daidaita alaka da gwamnatin mamayar Isra’ila.

Mustapha Yahi, sakatare-janar na National Democratic Rally (RND) ne ya bayyana haka a wata hira da ya yi da wakilin jaridar Al-Alam: inda yake cewa “Mun sake yin Allah wadai da ci gaba da ta’addancin isra’ila.

Abdelaali Hassani Cherif, shugaban kungiyar Movement of Society for Peace (MSP), ya jaddada bukatar karfafa hadin gwiwa na cikin gida don tinkarar zaluncin da kasashen yammaci da wasu kasashe ke yi a yankin t ahnayar goyon bayan matsayar Aljeriya kan batun Falasdinu.

Kusan shekaru uku da suka gabata, a cikin 2022, ‘yan majalisar dokokin Aljeriya sun kirkiro wani shiri na haramta duk wani yunkuri ko shiri na daidaitawa da Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments