Da safiyar yau Alhamis ‘yan gwgawarmaya daga Iraki sun harba jirage marasa matuki guda uku zuwa kudancin Falasdinu dake karkashin mamaya.
Harin na ‘yan gwgawarmayar Iraki ya shafi na’urorin hangen nesa na “Radar” dake yankin Dimona.
Sanarwar da ‘yan gwgawarmayar na Iraki su ka fitar ya ce wannan harin yana a matsayin martani ne ga kisan kiyashin da ‘yan sahayoniya suke yi wa Falasdinawa mata da kananan yara.
Tun farkon yakin Gaza ne dai ‘yan gwagwarmaya daga Iraki su ka shiga sahun masu kai wa manufofin HKI da na Amurka hare-hare da zummar taya Falasdinawa fada.
Irakawan suna amfani da jirage marasa matuki a mafi yawancin lokuta wajen kai wa manufofin HKI hare-hare, wasu lokutan kuma da makamai masu linzami samfurin “Ballistic”.