‘Yan gwagwarmaya a Iraki sun sha alwashin shiga yaki da Isra’ila matukar ta kai wa Lebanon hari

Kungiyar Islamic Resistance in Iraq, ta bayyana shirinta na yakar Isra’ila da Amurka idan gwamnatin mamaya ta yi gigin bude wani sabon yaki kan kasar

Kungiyar Islamic Resistance in Iraq, ta bayyana shirinta na yakar Isra’ila da Amurka idan gwamnatin mamaya ta yi gigin bude wani sabon yaki kan kasar Labanon.

Wani kwamandan kungiyar ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP a ranar Laraba cewa,  idan Isra’ila ta kai wani mummunan hari na soji kan Lebanon, to kuwa tabbas ba za su zama ‘yan kallo ba.

Kwamandan wanda ya nemi a sakaya sunansa ya kuma ce tuni kungiyar gwagwarmayar Musulunci a Iraki ta aike da kwararru da masu ba da shawara zuwa kasar Labanon.

A halin da ake ciki, masanin siyasar Iraki Ali al-Baidar ya yi gargadin cewa, duk wani babban yaki tsakanin Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Hizbullah ta Labanon “ba zai takaitu da Lebanon kadai ba.

Ya kara da cewa “A Iraki da kuma yankin, kungiyoyi masu dauke da makamai za su shiga arangama da Isra’ila da kuma Amurka da masu mara musu baya.”

Tun daga ranar 8 ga watan Oktoba ne dai kungiyar Hizbullah da Isra’ila ke ta musayar wuta da juna, jim kadan bayan da sojojin yahuadawan suka kaddamar da yakin kisan kiyashi a zirin Gaza bayan wani harin ba-zata da kungiyar gwagwarmayar Hamas ta Falasdinu ta kai.

Kungiyar Hizbullah ta lashi takobin ci gaba da kai hare-haren ramuwar gayya muddin gwamnatin Tel Aviv ta ci gaba da kai hare-hare a zirin Gaza, wanda kawo yanzu ya yi sanadin shahadar Falasdinawa kimanin  38,000, galibi mata da kananan yara, tare da jikkata wasu 87,266.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments