‘Yan Gwagwarmaya A Iraki Sun Kai Hari Da Makamai Masu Linzami Kan Sansanonin Sojin Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Islama ta kasar Iraki ta kai wani hari da makami mai linzami kan wani sansanonin sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila a cikin a yankunan

Kungiyar gwagwarmayar Islama ta kasar Iraki ta kai wani hari da makami mai linzami kan wani sansanonin sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila a cikin a yankunan Falasdinawa da ta mamaye.

Da jijjifin safiyar yau Litinin kungiyar ta kai hari da makamai masu linzami na al-Arqab a sassa daban-daban na yankunan Falastinawa da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta mamaye. Kawo yanzu dai babu wani rahoto kan asarorin da hakan ya haifar.

Da yammacin jiya Lahadi ne mayakan na Iraki suka kai wasu sabbin hare-hare kan wuraren na sojin Isra’ila.

A cikin wata sanarwa da ta fitar,  gamayyar kungiyoyin gwagwarmaya ta ce ta kai hari kan wasu sojojin Isra’ila a gabar kogin Jordan ta hanyar amfani da jirage marasa matuka.

Kungiyar masu fafutukar ta ce galibin jiragen sun kai farmaki kan wuraren da suke karkashin tsaro na Isra’ila, kuma tsarin makaman kariya na gwamnatin yahudawa ya kasa dakile yawancin jiragen.

“A ci gaba da tafarkinmu na tinkarar mamayar Isara’ila, da goyon bayan al’ummarmu a Gaza, da kuma mayar da martani ga kisan kiyashin da ‘yan ta’addan suka yi wa fararen hula Falasdinawa, da suka hada da yara, mata da tsofaffi, mayakan gwagwarmaya na sa kai a Iraki a safiyar Lahadi 22-9-2024, mun kai hari a wani wurin tsaro na sojin Isra’ila  a yammacin gabar kogin Jordan da ke cikin Falastinu da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta mamaye,  ta hanyar amfani da jirgin yaki mara matuki samfurin  ‘Al-Arfad’. Wanda kuma shi ne hari na biyar a ranar ta Lahadi.” in ji sanarwar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments