Yan gudun hijira 13 ne aka tabbatar da mutuwarsu a ranar 3 ga watan satumban da muke ciki bayan da kwalekwalensu ya nutse a kan hanyarsu ta zuwa ingila daga kasar Faransa ta hanyar ruwa.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa kwale-kwalen yana dauke da mutane fiye da 61 a lokacinda hatsarin ya auku a arewacin tekun Faransa.
Masu ceto sun ceci mafi yawan yan gudun hijirar da suke cikin kwalekwalen sai dai har yanzun akwai wasu mutane 12 suna jinya a asbitoci a kasar Faransa.
Ministan harkokin cikin gida na kasar Faransa ya bayyana al-amarin a matsayin abin bakinciki, ya kuma ziyarci wadanda abin ya shafa a arewacin kasar Faransa.