Yahudawa masu zanga-zanga sama da rabin miliyan ne suka fito kan tituna a duk fadin biranen Haramtacciyar Kasar Isra’ila, suna neman a kammala yarjejeniyar musayar fursunoni da kungiyar Hamas, biyo bayan wallafa hotunan fursunonin Isra’ila da aka kashe a zirin Gaza sakamakon harin bam da Isra’ila ta kai.
An fara gagarumar zanga-zanga a biranen Tel Aviv da Haifa, inda masu zanga-zangar suka bukaci a kammala yarjejeniyar musayar fursunoni, inda suka toshe hanya da kuma arangama da ‘yan sanda.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun tabbatar da cewa sama da masu zanga-zangar rabin miliyan ne suka fantsama kan tituna a ko’ina cikin birane domin neman a kammala yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas, yayin da tashar Channel 12 ta ce zanga-zangar da ake yi ita ce mafi girma tun daga lokacin da aka fara yaki kan Gaza.
Hukumar da ke kula da iyalai da maido fursunonin Isra’ila daga zirin Gaza ta tabbatar da cewa, adadin wadanda suka gudanar da zanga-zangar ya kai rabin miliyan a Tel Aviv, da kuma 250,000 a sauran garuruwan.
Dubban daruruwan yahudawa ‘yan share wuri zauna ne suka fito a yammacin ranar Asabar, a birnin Tel Aviv, daura da hedkwatar ma’aikatar tsaro ta Isra’ila, domin neman yarjejeniyar musayar fursunoni cikin gaggawa.
Da dama daga cikin yahudawan sun yi iamnin cewa, Netanyahu baya son tsayar day akin, saboda masaniyar da yake ita kan cewa, hakan yana nufin kawo karshen rayuwarsa ta siyasa kenanan a Ira’ila.