WHO: Masu Ciwon Koda 400 A Gaza Sun Mutu Saboda Rashin Magani

Hukumar lafiya ta duniya  (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu

Hukumar lafiya ta duniya  (W.H.O ) ta sanar da cewa rashin magani da na’urorin wanke koda a Gaza, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 400 masu fama da wannan cutar.

Hukumar lafiyar ta duniya ( w.h.o) ta kuma yi ishara da yadda ‘yan mamaya su ka lalata bangarorin da suke kula da cutuka na musamman a cikin asibitoci.

Ita ma hukumar lafiya ta Gaza ta bayyana cewa; masu fama da cutar koda a yankin suna fama da matsaloli na rashin Magani, kuma daruruwa daga cikinsu sun mutu saboda hakan.

Haka nan kuma ta  yi ishara da yadda mutane 400 daga cikinsu su ka rasu, da hakan yake nufin kaso 40% na adadin masu wannan cutar.

A gefe daya, ma’aikatar kiwon lafiyar ta Falasdinu ta yi tir da yadda ‘yan mamaya su ka kai wa asibitin “Durrah” na yara hari a gabashin birnin Gaza.

Haka nan kuma hukumar kiwon lafiyar ta Gaza, ta tabbatar da cewa hare-haren da ‘yan mamayar su ka kai wa dakin da yake kula da marasa lafiya na musamman a cikin asibitin kananan yaran, da kuma tashar samar da wutar lantarki a cikin asibitin.

Sanarwar hukumar lafiya ta Gaza ta ce, baya ga hana shigar da abinci da magani da ‘yan mamayar suke yi, suna kuma hana Falasdinawa ci gaba da rayuwa. Ita kuwa hukumar agaji ta “Red-Crecent” ta bayyana cewa; ‘Yan mamaya sun tafka laifukan yaki da su ka hada da kashe masu aikin agaji a cikin watan Maris.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments