A cikin makonnin baya-bayan nan manyan biranen kasar Faransa sun sheda gagarumar zanga-zangar nuna korafi kan karuwar matsalolin rayuwa ta fuskoki daban-daban, lamarin da ya fara daga korafin dalibai kan batun matsalolin da harkar ilimi ke fuskanta, daga bisani kuma zanga-zangar ta koma ta mutanen kasa da ke bayyana korafe-korafensu kan matsalolin rayuwa, da hakan ya hada da tashin farashin kayan masarufi, sakamakon karuwar farashin makamashi. Lamarin da ya kai ga yin taho mu gama tsakanin jami’an tsaro da kuma masu zanga-zanga a wasu birane.