Malam ya ci gabane da kawo mana yanda akaƙar aikin bawa da sakamakon da yake girba daga wannan aikin wato na azaba kamar yanda zaman da ya gabata ya kawo. Sannan kuma yaci gaba da bamu misalan ko wanne daga cikin su da kuma kawo mana ayoyin Alkur’ani da hadisan Manzon tsira da suke ayyada ra’ayi na Uku (Wato na cewa alaƙar dake tsakanin aikin bawa ko rashin aikinsa da har ya cancanci azaba alaƙa ce ta cewa kai tsaye Mutum da ya aikata aikin da ya cancanci azabar Allah ke yi masa) sai dai kawai sakamakon ita wannan duniyar ba gida ce da Mutum zai iya jin wannan azabar ba shi yasa bai ji. Amma daga lokacin da ya mutu ya koma wancan duniyar ta barzaku ko lahira a nan ne Mutum zai riski hakan.