Iran Kasa Mai Tsohon Tarihi Na Dubban Shekaru
Iran kasa ce mai tsohon tarihi da ke komawa zuwa ga dubban shekaru. Wuri ne da ke a matsayi alama ta tarihi da ci gaban dan adam na tsawon shekaru, ta yadda Iran ta kasance Daula mai karfi da ci gaba a dukkanin fuskoki na rayuwar dan adam dubban shekaru kafin haihuwar Annabi Isa.