Sanannen abu ne cewa Babu wani Daga cikin mahaifa da bai son ganin ɗan sa ya taso da Tarbiyya mai kyau. Sai dai lamarin ba kawai a Magana bane, yana buƙatar ilimi da masaniya Kan yanda mutum zai yi tarbiyyar mai kyau wanda matuƙar ya yi wa ɗan nasa da taimakon Allah tabbas zai taro mai kyawawan dabi’un. Daya daga cikin waɗannan marhalolin da yaro yake bukatar bada kulawa da lokaci da muhimmanci shine wannan lokacin da yaro kan kai Wanda yake yawan tambayoyi kuma yana jiran amsarsu daga mahaifan. Mu sani cewa Allah ta’ala ya bamu yara ne a matsayin amana , kuma mu muka zabi zamu karbi wannan amanar, sannan ilimi na Addini da na yau wato Misalin ilimin sanin halayyar dan Adam ya tabbatar da hanyoyin da matukar mun bi yaro zai taso mai tarbiyya abin alfahari a cikin al’umma abin alfahari ga iyayennsa.