Zaman babban taron zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 81 na 2026, ya zo ne a daidai lokacin da duniya ta samu kanta a cikin wani mummunan yanayi, sakamakon haifar da tashe-tashen hankula da Amurka ke jagoranta a duniya, musamman ma tun bayan kaddamar da harin hadin gwiwa tsakaninta da Isra’ila a kan Iran, da kuma mummunan da sakamako da hakan ya haifar wa duniya baki, wanda shi ne yafi daukar hankula a cikin mafi yawan jawaban da aka gabatar a taron.