Turkiyya Ta Gargadi Cyprus Kan Taimakon Haramtacciyar Kasar Isra’ila A Yakin Gaza

Gwamnatin Turkiyya ta gargadi kasar Cyprus kan taimakawar da take yi ga haramtacciyar kasar Isra’ila a yakin da ta kaddamar kan Falasdinawa Ministan Harkokin Wajen

Gwamnatin Turkiyya ta gargadi kasar Cyprus kan taimakawar da take yi ga haramtacciyar kasar Isra’ila a yakin da ta kaddamar kan Falasdinawa

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tabbatar da cewa: Kasar Cyprus ta zama cibiyar ayyukan kai hare-haren gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila kan Gaza, yana mai gargadin ta da ta guji kasancewa wani bangare na rikici.

Fidan ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na HaberTurk na kasar Turkiyya a yau Talata, yana mai jaddada cewa: Suna yawan ganin rahotannin sirri da suke nuni da cewa wasu kasashe na amfani da gwamnatin Cyprus ta Girka a kudancin Cyprus a matsayin sansaninsu musamman wajen gudanar da ayyukansu na wuce gona da iri kan Gaza. Fidan ya kara da cewa: Lokacin da Cyprus ta shiga cikin yake-yaken da ake yi a yankin Gabas ta Tsakiya, to babu makawa wannan wutar yake-yake za ta zo ta same ta, kuma tun da Turkiyya ta hada yankin kasa daya da Cyprus, to tana shawartarta da ta nisanci shiga rikicin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments