Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana gamsuwarsa da yadda tattaunawa tsakanin kasarsa da Iran ke gudana, yana mai bayyana ta a matsayin mai matukar kyau.
Da yake magana da manema labarai a fadar White House jiya litinin, Trump ya ce tattaunawa da akayi da jami’an Iran sun yi matukar inganci.
A ranar 12 ga watan Afrilu ne aka gudanar da zagayen farko na tattaunawar wacce ba ta kai tsaye ba tsakanin Iran da Amurka a shiga tsakanin kasar Oman a birnin Muscat.
Haka zalika a ranar Asabar 19 ga watan Afrilu bangarorin sun yi wa ta biyu a birnin Rome na kasar Italiya, a shiga tsakanin kasar Oman.
kasashen biyu sun bayyana kwarin gwiwar cewa za a ci gaba da tattaunawa, inda za a sake gudanar da mataki na gaba a kasar Oman a ranar Asabar mai zuwa.
Kafin nan kwararu daga kasashen na Amurka da Iran zasu hadu a kasar Oman a gobe Laraba inda zasu tattauna game da shirin nukiliyar na Iran na zaman lafiya.