Tinubu ya karfafa ayyukan kula da ayyukan gandun daji 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karbi kundin bayanan kwamitin fadar shugaban kasa akan duba lamuran dabbobi da zummar samar da gyara a bangaren, sabodar sama

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya karbi kundin bayanan kwamitin fadar shugaban kasa akan duba lamuran dabbobi da zummar samar da gyara a bangaren, sabodar sama da damammaki musamman wajen magance matsalar rikice-rikicen manoma da makiyaya da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Mai magana da yawun shugaban kasar ne bayo Onanuga ya ba da wannan sanarwa a shafinsa na X wadda aka fi sani da twitter.

Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu, ya karbi rahoton kwamitin fadar shugaban kasa kan aiwatar da sauye-sauyen kiwon dabbobi daga hannun mataimakin shugaban kwamitin Farfesa Attahiru Jega a fadar sa dake babban birnin kasar Abuja.

Shugaba Tinubun ne ke shugabantar kwamitin amma tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasar ne Attahiru Jega, ke jagorantar dukkanin kaikomon da ya gudana.

Wani bangare na aikin kwamitin shine samar da hanyoyin kafa ma’aikatar kula da dabbobi.

A yayin da Jaridar Premium Times da ake wallafawa a kasar ta ruwaito sanarwar da shugaban ya fitar na shirin samar da ma’aikatar domin magance matsaloli da sukayi katutu a bangaren.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments