Tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta yi magana kan laifuffukan yaki da bangarorin da suke yaki da juna suka tafka a kasar
Tawagar bincike ta Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta sanar da cewa: Bangarorin biyu da suke rikici da juna a Sudan sun aikata munanan ayyukan take hakkokin dan Adam wadanda zasu iya zama laifukan yaki, tana mai jaddada yin kira ga hukumomin Sudan da su ba da hadin kai ga kotun hukunta manyan laifuka ta duniya.
Tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana a cikin wani rahoto da ta fitar cewa: Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun kaddamar da hare-hare na kabilanci a yankin Darfur, kuma bangarorin biyu masu fadan suna kame mutane ba bisa ka’ida ba, da azabtarwa, da cin zarafi ta hanyar yin fyade ga mata, baya ga kai hare-haren wuce gona da iri musamman ta sama kan fararen hula da kuma kai hare-hare kan makarantu, asibitoci, hanyoyin sadarwa, da cibiyoyin ruwan sha da na wutar lantarki.
Tawagar ta kuma yi kira ga sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa da su dakatar da kai hare-hare kan fararen hula ba tare da wani sharadi ba, tare da ba da shawarar tura wata runduna mai zaman kanta da za ta kare al’ummar kasar, yayin da babu wani karin haske daga hukumomin Sudan kan rahoton da aka fitar na cin zarafin da ke faruwa a kasar.