Kakakin rundunar sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e ya sanar da aiwatar da hare-haren soji guda biyu tare da jiragen yaki marasa matuka ciki a kan birnin Yaffa da aka mamaya da Umm al-Rashrash da ke kudancin Falasdinu da aka mamaye.
A cikin wata sanarwa da aka watsa ta gidan talabijin kakakin rundunar sojin kasar ta Yemen ya bayyana cewa: Sojojin saman Yemen sun kai hari da jirgin sama maras matuki ciki kan sansanin sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke yankin Yaffa da aka mamaye, sannan kuma sun kai hari kan wani sansanin soji a yankin Umm al-Rashrash Eilat. da jiragen sama marasa matuka ciki kirar Sammad guda hudu.
Birgediya Janar Sari’e ya tabbatar da cewa: Hare-hare sun isa wurin da aka harba su, yana mai cewa: Hare-haren suna zuwa ne a matsayin tallafa wa al’ummar Falastinu da Lebanon da kuma jaddada goyon baya ga gwagwarmayar Falasdinu da Lebanon.