Sojojin Yemen sun harbo wani jirgin saman yakin Amurka (MQ_9) a gundumar Ma’arib na kasar
Sojojin Yemen sun sanar da harbo wani jirgin saman Amurka (MQ_9) a gundumar Ma’arib, tare da jaddada cewa za su kai hare-hare kan duk wani yunkurin sojojin Amurka da Birtaniya a yankin musamman a fannin ayyukan teku.
A wata sanarwa da rundunar sojin Yemen ta fitar ta jaddada cewa: A fagen ci gaba da taimakawa al’ummar Falastinu da ake zalunta da kuma ‘yan gwagwarmaya da suke fafatukar kare kansu da kuma mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri na Amurka da Birtaniya da suke yi kan kasar Yemen, sojojin tsaron saman Yemen sun yi nasara tare da taimakon Allah Madaukakin Sarki wajen harbo wani jirgin saman Amurka MQ-9 a lokacin da yake gudanar da wani mummunan aiki a sararin samaniyar yankin gundumar Ma’arib. Sojojin kasar ta Yemen sun kara da cewa: Wannan jirgin shi ne na takwas daga cikin irin wannan nau’in da sojojin Yemen suka yi nasarar harbowa a yayin yakin da suke da jihadi mai tsarki na goyon bayan Gaza.