Sojojin Yemen Sun Kai Hare-Hare Kan Jiragen Ruwa Da Suke Tafiya Haramtacciyar Kasar Isra’ila

Sojojin Yemen sun kai hari kan wani jirgin ruwa a tekun Bahar Maliya da mashigar Bab al-Mandab Rundunar sojin kasar Yemen ta sanar da aiwatar

Sojojin Yemen sun kai hari kan wani jirgin ruwa a tekun Bahar Maliya da mashigar Bab al-Mandab

Rundunar sojin kasar Yemen ta sanar da aiwatar da wani harin soji kan wani jirgin ruwa a tekun Bahar Maliya, a matsayin mayar da martani ga kisan kiyashin da makiya yahudawan sahayoniyya suke yi kan al’ummar Falastinu a Zirin Gaza.

Rundunar sojin kasar ta Yemen ta kara da cewa: Sojojin ruwa, da na sama, da kuma sojojin masu kula da harkar makamai masu linzami sun kaddamar da wasu hare-haren hadin gwiwa kan jirgin ruwa (Charysalis) a tekun Bahar Maliya da Bab al-Mandab.

Sanarwar ta bayyana cewa: Harin da aka kai wa jirgin ya zo ne saboda kamfanin jirgin ya saba wa matakin hana shiga tasoshin ruwa na Falasdinu da ke mamaye da su.

Kamar yadda sanarwar ta fayyace cewa: An kai hare-haren ne sau biyu, na farko a tekun Bahar Rum, na biyu kuma a Bab al-Mandab, tare da wasu makaman ballistic da na ruwa da kuma jiragen sama marasa matuka ciki.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa: Ayyukan sojojin kasar Yemen ba za su tsaya ba, matukar dai ba a daina kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza tare da dakatar da yaki da ake yi kan al’ummar Falastinu a Zirin Gaza ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments