Sojojin Yemen Sun Kai Hare Hare Guda Biyu Kan Jiragen Ruwan Kasuwanci A Tekun Maliya

Kakakin sojojin kasar Yemen ya bada sanarwan cewa sojojin kasar sun cilla makamai kan wani jirgin ruwan kasuwanci mallakin Amurka a cikin tekun maliya da

Kakakin sojojin kasar Yemen ya bada sanarwan cewa sojojin kasar sun cilla makamai kan wani jirgin ruwan kasuwanci mallakin Amurka a cikin tekun maliya da kuma wani wanda yake kan hanyarsa ta zuwa HKI a jiya Alhamsi.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Bugediya Janar Yahaya Saree kakakin sojojin kasar Yemen ya na fadar haka a jiya Alhamis, ya kuma kara da cewa jiragen ruwan sun sabawa dokar gwamnatin kasar Yemen ta hana dukkan jiragen ruwa masu zuwa HKI daga ko ina wucewa ta tekun maliya ko tekun aden ko tekun Arabia.

Gwamnatin kasar ta Yemen ta dauki wannan matakin ne don tallafawa falasdinawa wadanda HKI take masu kissan kiyashi a zirin Gaza. Har’ila yau da kuma maida martani kan hare haren da sojojin Amurka da Burtaniya suke yi a kan mutanen kasar ta Yemen.

Labarin ya kara da cewa jiragen kasuwancin da abin ya shafa sun hada da OLYMPIC SPIRIT na daukar man fetur kuma mallakin kasar Amurka. Sun kuma cilla makamai masu linzami da jiragen drones har 11 kan jirgin.

Na biyun shi ne jirgin kasuwanci mai suna ST.JOHN saboda ya sabawa dokar hana zuwa HKI wacce kasar ta Yemen ta kafa. Shi ma sojojin sun yi amfani da makamai masu linazami da kuma ‘drones’ don tarwatsa shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments