Sojojin HKI Suna Ci Gaba Da Kissan Kare Dangi A Gaza Duk Tare Da Hare Haren Da Take Kaiwa Kan kasar Lebanon

Sojojin HKI a Gaza suna ci gaba da kissan kiyashin da suka saba yi kimani shekara guda da ta gabata a Gaza. Kamfanin dillancin labaran

Sojojin HKI a Gaza suna ci gaba da kissan kiyashin da suka saba yi kimani shekara guda da ta gabata a Gaza.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya bayyana cewa a garin Addarj dake arewacin zirin gaza, falasdinawa 3 ne aka tabbatar da shahadansu a hare haren sojojin HKI  a yau Lahadi.

Haka ma a wata anguwar a garin Nusairat na tsakiyar zirin gaza sojojin HKI sun kai hare hare wadanda suka jiwa falasdinawa da dama raunuka, sannan sun kara rusa gidajen  Falasdinawa a yankin.

Sai kuma a unguwar Al -juninah na gabacin Rafah daga kudancin Gaza sojojin yahudawan sun kai hare hare inda suka kai bafalasdine guda ga shahada.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Gaza ta bayyana cewa ya zuwa yanzu Falasdina 41,586 suka yi shahada tun ranar 7 ga watan Octoban shekarar ta 2023, a yayin da wasu falasdinawa 96,210 suka ji Rauni, mafi yawansu mata da yara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments