Shugabar Jami’ar Columbia ta yi murabus bayan zanga-zangar dalibai masu goyon bayan Falasdinu

Shugabar Jami’ar Columbia Nemat Minoosh Shafiq ta yi murabus daga mukaminta biyo bayan zanga-zangar da dalibai suka yi na nuna goyon bayan Falasdinu da Zirin

Shugabar Jami’ar Columbia Nemat Minoosh Shafiq ta yi murabus daga mukaminta biyo bayan zanga-zangar da dalibai suka yi na nuna goyon bayan Falasdinu da Zirin Gaza, wanda aka fara watanni 4 da suka gabata a harabar jami’ar a birnin New York.

A rahoton tashr Al-Mayadeen, shugabar jami’ar Columbia Nemat Minoosh Shafiq ta yi murabus daga mukaminta a yau sakamakon zanga-zangar daliban da aka fara a watan Afrilun da ya gabata a harabar jami’ar New York don nuna goyon baya ga Falasdinu da aka mamaye da zirin Gaza.

Murabus din shugabar jami’ar Columbia ya zo ne shekara guda bayan nada ta kan wannan mukami da kuma sukar da ta sha a watannin da suka gabata dangane da yadda ta fuskanci zanga-zangar daliban da suka yi Allah wadai da yaki da kisan kiyashi na gwamnatin sahyoniyawan a zirin Gaza.

Nemat Minoosh Shafiq ta kira ‘yan sandan New York da su tarwatsa daliban da suka gudanar da zanga-zangar da daliban suka yi, lamarin da yasa ta fuskanci kakkausar suka a cikin jami’ar, da hakan ya hada da malamai da ma’aikata; Domin ‘yan sanda sun kama dalibai masu yawa tare da cin zarafinsu.

Shugabar Jami’ar Columbia ya fara ayyukanta a matsayinta na shugabar jami’ar a watan Yulin shekarar da ta gabata, kuma a ranar 9 ga watan Oktoba, kwanaki biyu bayan fara yakin Isra’ila a Gaza, ta fitar da wata sanarwa inda ta bayyana goyon bayanta ga gwamnatin sahyoniya.

A watan Nuwamban bara, jami’ar ta dakatar da ayyukan kungiyar “Students for Justice in Palestine (SJP)” bisa hujjar shirya ” zanga-zangar da ba ta da izini “.

A cikin watan Afrilun bana, Shafiq ta fuskanci zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinawa a harabar jami’ar inda ta nemi ‘yan sanda da su taimaka, inda aka kama daruruwan dalibai.

Daruruwan malaman jami’ar Columbia sun nuna  adawa da matakin da shugabar jami’ar ta dauka na kame daliban da ke gudanar da zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments