Shugaban Turkiyya Ya Ce Duk Mai Ba Da Makamai Ga ‘Yan Sahayoniyya Ya Yi Tarayya Da Su A Laifukansu

Shugaban kasar Turkiyya ya bayyana cewa: Duk wanda ke bai wa haramtacciyar kasar Isra’ila makamai, yana da hannu a tashe-tashen hankulan da take tayarwa a

Shugaban kasar Turkiyya ya bayyana cewa: Duk wanda ke bai wa haramtacciyar kasar Isra’ila makamai, yana da hannu a tashe-tashen hankulan da take tayarwa a Gabas ta Tsakiya

Shugaban kasar Turkiyya Rajab Tayyib Erdogan ya bayyana cewa: Kasashen Yamma da suke bai wa gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila makaman da take amfani da su wajen aiwatar da kisan kiyashi a Gaza da Lebanon, suna tarayya da ita a muggan laifukan da take aiwatarwa kan Falasdinawa da al’ummar Lebanon.

Erdogan ya jaddada cewa: Wadanda suke ba da makamai ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suna tarayya da yahudawan sahayoniyya a ci gaba da cin zarafin al’ummar Falasdinu da Lebanon.

Shugaban kasar ta Turkiyya a cikin jawabinsa ya jaddada cewa: Akwai wadanda ke jin dadin kashe yara tun suna kanana da mata, lamarin da ya zo daidai da ci gaba da goyon bayan kasashen yammacin duniya ga cibiyar kashe-kashe da aiwatar da kisan kiyashi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments