Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: Ƙarfin ƙasar Iran da tsaro sun dogara ne kan karfin sojojinta
Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya dauki karfi da tsaron kasar a yau a matsayin irin karfin da sojojin suke da shi.
A yayin ganawarsa da manyan kwamandojin sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian ya yi nuni kan muhimmancin tsarin rundunar sojin kasa da kuma yadda ake gudanar da ayyukanta ga sauran fannonin gudanarwa a cikin kasar, kuma ya kara da cewa: A cikin ilimin gudanarwa, ana fitar da mafi inganci kuma mafi gwazo daga tsarin soji, sannan kuma a koyar tare da yin nazarinsa a jami’a, sannan kuma sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran suna da tsari na tushe da zasu iya koyar da kwarewar su ga fannoni na sassa daban-daban.
Shugaban ya kuma jaddada cewa: Dole ne a yi amfani da rundunar soji wajen yi wa jama’a hidima, ba wai amfani da su wajen kashe mata da kananan yara da kuma fararen hula ba, ya kuma yi nuni da cewa masu yi wa ‘yancin dan’Adam hidima da kare tsarin dimokuradiyya suna tsayin daka a fagen rajin kare hakkokin dan Adam, a halin yanzu suna cikin halin tsaka mai wuya sakamakon yadda gwamnatocinsu suka rikide masu goyon bayan ayyukan ta’addanci tare da goyon bayan aiwatar da kashe-kashen gilla kan mata da kananan yara, musamman ta hanyra jefa muggan bama-bamai a kan al’ummar Gaza.