Shugaban Kasar Iran Ya Ce: Duk Mai Tunanin Za A Iya Murkushe Gwagwarmaya, To Yana Cikin Rudu

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Duk wanda yake tunanin cewa za a ruguza tutar gwagwarmaya ta hanyar kashe-kashen gilla, to lallai ya kuskure Shugaban

Shugaban kasar Iran ya bayyana cewa: Duk wanda yake tunanin cewa za a ruguza tutar gwagwarmaya ta hanyar kashe-kashen gilla, to lallai ya kuskure

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce: Idan ma’abuta girman kai suna tunanin cewa za a ruguza tutar gwagwarmaya ta hanyar aiwatar da kashe-kashen gilla kan jagororin kungiyoyin na gwagwarmaya, to tabbas suna cikin rudu da tafka mummunan kuskure.

A cikin wata sanarwa da ya aike wa wakilin gidan talabijin na Al-Manar na kasar Lebanon Shugaba kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Ma’abota girman kai suna gabatar da ‘yan ta’adda a matsayin masu ceton al’umma da kuma daukan mutanen da suke goyon bayan wadanda aka zalunta a matsayin ‘yan ta’adda kuma idan masu girman kai sun kasance suna zato aiwatar da kashe-kashen gilla kan jagorori da                                                                                                                                                                  mayakan kungiyoyin gwagwarmaya da suke yaki domin murkushe zalunci da ayyukan wuce gona da iri  da barna, shi ne kawo karshen fada da girman kansu, to lallai sun yi babban kuskure.

Shugaban ya ci gaba da cewa: Za su tsaya tsayin daka wajen yakar zalunci da aikata laifuka da dukkan karfinsu. Kuma suna da Yakini da amincin cewa: Dukkanin ’yan’uwansu da daukacin al’ummar musulmi da ‘yantattun al’ummar duniya ba za su kyale ana gudanar ayyukan zalunci ba tare da kalubalantarsa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments