Shugaban Kasar Iran Ya Bayyana Manufar Kasarsa Da Shirin Kare Muradunta A Duk Wata Yarjejeniya

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada

Shugaban kasar Iran ya jaddada cewa: A shirye suke su cimma yarjejeniya yayin da suke kiyaye muradun kasarsu

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya jaddada cewa: Iran a shirye take ta cimma matsaya bisa kayyade tsare-tsare tare da kiyaye moriyar kasarta, amma idan ba ta son yin shawarwari da ta daga kan matsayinta, tare da ci gaba a kan tafarkinta. Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya ce: Babu kyakykyawan fata kuma ba za a fitar da rai ba.

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian da yake jawabi a taron da gwamnonin kasar suka yi a ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar a yau, ya yi jawabi kan shirin tattaunawa ba na kai tsaye ba da Amurka, yana mai cewa: Tun da fari gwamnatin Iran ta jaddada cewa tana kokarin karfafa dangantakar siyasa da tattalin arziki da kimiyya da al’adu da sauran kasashe, musamman ma kasashen musulmi da na makwafta. Iran tana kuma neman kyakkyawar mu’amala da sauran kasashe bisa mutunta juna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments