A rana ta biyu ta ziyarar aiki da shugaban kasar Iran Sayyid Ibrahim Ra’isi yake yi a kasar Pakisran a yau Talata ya ziyarci kushewar Muhammad Ali Jinah a garin Sind dake gundumar Karachi wanda shi ne ya samar wa da kasar ‘yanci.
Shugaban na Iran ya fara ziyarar aiki ne a kasar Pakistan a jiya Litinin inda yake ganawa da manyan jami’an gwamnatin kasar domin bunkasa alaka a tsakanin kasashen biyu masu makwabta da juna.
Shi dai Muhammad Ali Jinah ya taka gagaruwar rawa a gwgawarmayar samar wa kasar ta Pakistan ‘yanci daga India sannan kuma ya zama jagoranta na farko bayan ‘yanci.
A gefe daya jami’ar Karachi ta girmama shugaban kasar na Iran ra hanyar ba shi digirin digirgir.
Shugaban jami’ar ta Karachi Khalid Iraki ne ya mika wa shugaba Ibrahim Ra’isi shaidar digirin na uku na girmamawa a wani kwarya-kwaryar biki da aka yi.