Shugaban gwamnatin kasar Lebanon Najib Mikati ya ce; Yadda “Israila’ take tsananta kai wa unguwar Dhahiya hare-hare yana nuni da cewa, ba su son tsagaita wutar yaki.
Najib Mikati ya kuma ce Yadda Isra’ila take rusa birane da kauyukan Lebanon, manuniya ce akan cewa ba ta son tsagaita wuta balle kuma aiki da kudirin MDD mai lamba 1701.
Shugaban gwamnatin Lebanon din ya bayyana haka ne dai a yau Juma’a a lokacin da ya gana da kwamadan dakarun MDD na zaman lafiya a Lebanon ( UNIFIL), a fadar gwmanati dake birnin Beirut.
Najib mikati ya kuma fadawa janar Aroldo Lazaro cewa Lebanon a shirye take ta yi aiki da kudurin na MDD da dukkanin bangarorinsa.
Har ila yau Najib Mikayi ya yi tir da yadda sojojin HKI suke kai wa dakarun MDD hare-hare a kudancin Lebanon da kuma barazanar da suke yi musu.
A nashi gefen janar Aroldo Lazaro ya yi wa shugaban gwamnatin ta Lebanon bayani akan wahalar da suke sha, saboda yadda “Isra’ila” take yi musu barazana.